An ceto ′yan ci rani a gabar tekun Italiya | Labarai | DW | 24.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An ceto 'yan ci rani a gabar tekun Italiya

Sama da mutane 2,000 ne jami'an da ke kula da gabar tekun Italiya suka ceto rayuwasu a wannan juma'a, wani jirgin ruwa makare da 'yan gudun hijira ne ke kokarin ribtawa da su cikin teku

Sama da mutane dubu biyu ne jami'an da ke kula da gabar tekun Italiya suka ceto rayuwasu a wannan juma'a, wani jirgin ruwa makare da 'yan gudun hijira ne ke kokarin ribtawa da su cikin teku.

A kokarinsu na tsallakawa zuwa Turai ta barauniyar hanya, a cikin wata sanarwa da hukumomin da ke kula zirga-zirga a tekun, sun ce cikin kasa da sa'oi 48, an yi nasarar ceto rayuwar mutane sama da dubu goma sha biyu. Hadin gwiwar jiragen ruwa na likitocin kasa da kasa da na sojin ruwan kasar Italiya, hada da jiragin ruwa na gamaiyar iyakokin kasashen Turai ne suka gudanar da aiyyukan ceto na musamman ga 'yan gudun hijiran da ke neman salwanta a teku.