An cafke wani dan IS a Najeriya | Labarai | DW | 09.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An cafke wani dan IS a Najeriya

Rahotanni daga Abuja fadar gwamnatin Najeriya na nuni da cewar hukumar tattara bayanan sirri ta kasar ta tsare wani mutum da ake zargi da yi wa mutane rijistar shiga kungiyar IS.

Jami'an sojojin Najeriya

Jami'an sojojin Najeriya

Jawabin danke dan kungiyar IS din ya zo ne bayan kwashe shekara daya da jagoran kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya nuna goyon bayansa ga kungiyar ta IS. Bangaren tsaro na DSS sun ce an sami nasarar cafke Abdulsalam Yunusa a yayin da yake kokarin tafiya Libiya domin haduwa da mayakan IS. Kazalika Jami'an tsaron DSS sun ce mai yi wa mutanen rijistar shiga IS ya shaida musu cewar akwai 'yan Najeriya biyu da yanzu haka suke samun horo a Libya. Wannan dai shi ne karon farko da Jami'an tsaron Najeriya suka sami nasarar cafke wasu da ake zaton suna da alaka da kungiyar mayakan IS da kuma ke arcewa zuwa Libya don shiga kungiyar gadan-gadan.