1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An cafke Carles Puigdemont a Jamus

Abdourahamane Hassane
March 25, 2018

'Yan sanda na Jamus sun cafke tsohon shugaban Kataloniya Carles Puigdemont a kan iyakar Denmark da Jamus.

https://p.dw.com/p/2uwQh
Carles Puigdemont
Hoto: picture-alliance/AP/O. Matthys

Carles Puigdemont wanda ke a karkashin dokar kasa da kasa da Spain ta gabatar na a kamashi ya isa kan iyakar Danmark da Jamus ta cikin mota a Schleswig Holstein. Tun farko a ziyarar da ya kai a kasar Finland 'yan sandar sun nemi karin bayyani a game da buktar a kamashi. A ranar Juma'a da ta wuce ce wani alkali a Spain ya ba da umarnin kame wasu 'yan awaren guda biyar na Kataloniya saboda yunkurin da suka yi na neman a raba Spain biyu a ciki har da Carles Puigdemont.