An bude wuta a kan jami′an sa ido na kungiyar OSCE a Ukraine | Labarai | DW | 20.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An bude wuta a kan jami'an sa ido na kungiyar OSCE a Ukraine

Ma'aiakatan na kungiyar suna rangadin sanya ido ne a kan yarjejeniyar tsagaita wuta a gabacin Ukraine.

Masu sa ido na kungiyar tsaro da hadin kai a Turai OSCE sun ce wasu mutane cikin kayan sarki sun bude wuta a kan wani ayarin motocinsu a gabacin Ukraine. Ayarin dai na masu sa ido ne a kan shirin tsagaita wuta a yankin da ke fama da rikici da ke kusa da garin Maryinka. Sai dai ba wanda ya jikkata a wannan lamari. Yankin mai nisan kilomita 15 yamma da Donetzk tungar 'yan aware, yana karkashin ikon sojojin Ukraine ne. Tun bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wutar a farkon watan Satumba ake karya ka'idojinta. Alkalumman da Majalisar Dinkin Duniya ta bayar sun nuna cewa mutane kimaninn 1000 aka kashe a gabacin Ukraine tun bayan amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta a hukumance.