1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An bude Taron kotun ICC na shekara

November 17, 2016

Bude taron kotun hukuntan manyan laifukan ta kasa da kasa wato ICC na shekarar bana ya zo a dai-dai lokacin da kasahen duniya da dama ke kaurace mata a bisa nuna rashin gamsuwarsu da yadda take tafiyar da aikinta.

https://p.dw.com/p/2SrAu
Germain Katanga ICC Den Haag Urteil 23.05.2014 Opfervertreter
Hoto: picture-alliance/dpa

Yawan kasashen da ke daukar matakin ficewa daga kotun kasa da kasa mai hukunta manyan laifuka na karuwa. A baya-bayan nan wata sanarwar ma'aikatar harkokin wajen Rasha a birnin Mosko ta ce Shugaba Vladimir Putin ya amince da dokar janye wakilcin kasarsa daga kotun da ke birnin The Hague. Labarin ya zo ne a wannan Laraba a daidai lokacin da kotun ta fara babban taronta na shekara-shekara inda batun janye wakilcin wasu kasashen Afirka ya mamaye ajandar taron. 

Babban zauren taron birnin The Hague na kasar Holland ya cika da wakilai daga kasashe 124 da suka hada da 'yan shari'a da jami'an gwamnati. Duk kasashen dai sun rattaba hannu kan kudurin birnin Rom da ke zama tushen yarjejeniyar da ta kafa ginshikin fara aikin kotun ta duniya a shekarar 2002. Matakin ficewa daga kotun da wasu kasashen Afirka uku suka dauka ya mamaye taron kasashe membobin kotun na wannan shekara. Sai dai babbar mai shigar da kara ta kotun Fatou Bensouda ta ce ai babu wani abin damuwa.

"Duk da labaran da ake watsawa masu daukar hankali, wannan ba wata matsala ba ce ga kotun, to amma komabaya ne ga kokarinmu na samar da wanzuwar zaman lafiya tare da adalci a duniya."

Wladimir Putin
Hoto: picture-alliance/AP Photo/M.Schreiber

Kasashen Afirka ta Kudu da Burundi da kuma Gambiya da ke zama kasar haihuwar Fatou Bensouda suka janye daga kotun suna masu zargin kotun da baki biyu da kuma ta yi setin akalarta a kan laifukan yaki a Afirka kadai. To amma kowace kasa a cikinsu na da dalilanta na ficewa daga kotun. Ga misali 'yan siyasar Burundi na karkashin wani bincike na baya bayan nan.
Sai dai Fatou Bensouda ba ta nuna gajiyawa ba wajen lissafa irin nasarorin da aka samu tana mai nuni da wasu kararraki 10 da ke gabanta da kuma watakila wasu sabbi da za a shigar.

"Mun fara binciken farko kan wasu kararraki guda 10 da suka shafi kasashen Afghanitan da Burundi da Kwalambiya da aikace-aikacen sojojin Birtaniya a Iraki, da yankin Falasdinu da Najeriya da Ukraine da Komoros da kuma Gabon. Wannan shi ne abin da muke kai yanzu sai kuma wani kara da wata kasa Afirka memba a kotun ta shigar mana."

Akwai wasu zarge-zarge kwarara a kan rundunar sojin Amirka da ma'aikatan hukumar leken asirin  Amirka ta CIA musamman hanyoyin rashin imani da azabtarwa wajen neman bayanai daga firsinoni a Afghanistan da wasu gidajen kurkuku na sirri a kasashen Poland da Lisuwaniya da Romaniya. Masu shigar da karar na kuma sa ido kan yaki tsakanin Jojiya da Rasha game da kudancin Ossetia da mamaye yankin Kirimiya da kuma rikicin Gabacin Ukraine.

Südafrika Präsident Jacob Zuma
Hoto: Reuters/P. Bulawayo


Gwamnati a Mosko ta fusata saboda haka ta janye daga yarjejeniyar birnin Rom, sai dai matakin ba zai yi illa ga aikin kotun ba, domin tun farko Rasha ba ta rattaba hannun kan yarjejeniya aikin kotun ba. A saboda haka babban kwamishinan kare hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya Yerima Zeid al-Hussen dan kasar Jodan ya yi kira ga kasashen membobin kotun duniya kamar haka.

"Ku dage kan kudurin Rom da kuma wannan kotu. Watakila akwai nakasu a tsare-tsare da kuma yadda take tafiyar da aikinta, amma a yanzu ita ce kotun mafi kyau da muke da ita."

Wakilai a taron na da lokaci har zuwa ranar Alhamis ta makon gobe na dinke barakar da ke akwai in ba haka ba to ci gaba da wanzuwar kotun ta duniya na cikin hatsari.