An bude taron kolin EU kan samar da aikin yi | Labarai | DW | 24.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An bude taron kolin EU kan samar da aikin yi

Shugabannin tarayyar Turai da ke taron kolin yini biyu a birnin Brussles za su duba hanyoyin magance matsalar yawan marasa aikin yi a cikin kasashen kungiyar.

Shugabannin kasashen kungiyar tarayyar Turai sun bude taron kolinsu na yini biyu wanda cece-kuce game da leken asirin da ake zargin Amirka ta yi wa shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ya mamaye shi. Tuni dai shugannin EU suka nemi sanin gaskiyar lamarin daga gwamnatin Amirka. A gun taron shugabannin na tarayyar Turai za su kuma tattauna game da matsalar yawan marasa aikin yi da ta yi wa musamman matasan nahiyar katutu. Alkalumma sun yi nuni da cewa tarayyar EU dake zama wata kungiyar cinikaiya mafi girma a duniya, yawan marasa aikin yi a tsakanin matasa 'yan kasa da shekaru 25 da haihuwa ya kai kashi 23.3 cikin 100. Ko da yake shugabannin za su yi tattaunawa mai tsawo a kan wannan matsala amma ba wanda ya hango mafita daga matsalar ba saboda basussukan dake kan kasashen kungiyar.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu