1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a gudanar da babban zabe a Libya

Abdul-raheem Hassan
June 18, 2026

Jiga-jigan da ke ja in ja a gwamnatin Libya sun cimma matsaya kan gudanar da zabe don kawo karshen rikicin siyasa da ya dade yana addabar ci gaban kasar.

https://p.dw.com/p/5FfyJ
Mata suna shewa da tutar Libya a birnin Tripoli a shekarar 2020
Mata suna shewa da tutar Libya a birnin Tripoli a shekarar 2020Hoto: Mahmud Turkia/AFP

Sanarwar ta hadin guiwa ta zo ne sa'o'i kadan kafin shugabar tawagar Majalisar Dinkin Duniya a Libiya Hanna Tetteh ta gabatar da jawabi ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kan ci gaban da kasar ta samu a baya-bayan nan.

Shugabannin manyan cibiyoyin gwamnatin kasar sun amince da ci gaba da shirye-shiryen zaben shugaban kasa da na majalisar dokoki, bayan tattaunawa da aka yi domin warware sabanin da ya hana gudanar da zabe tun a 2021.

Majiyoyi sun ce bangarorin sun kuma jaddada muhimmancin hadin kai da samar da yanayin tsaro, don tabbatar da sahihin zabe a watan Febrairun 2027.

Libya ta shafe shekaru tana fama da rarrabuwar kawuna da gwagwarmayar siyasa tun bayan hambarar da tsohon shugaban kasar, Muammar Gaddafi a shekarar 2011. Ana fatan sabon yarjejeniyar za ta taimaka wajen kafa gwamnatin da za ta samu amincewar dukkannin bangarorin da ke gaba da juna.