An kulla yarjejeniyar sulhu a Libiya | Labarai | DW | 17.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kulla yarjejeniyar sulhu a Libiya

Bangarorin da ba sa ga muciji da juna na kasar Libiya sun rattaba hannu a kan jadawalin tabbatar da zaman lafiya da Majalisar Dinkin Duniya take shiga tsakani.

Wakilan da suka futo daga cikin majalisar kasar da ke adawa da juna sun sanya hannu ne a kan jadawalin tsarin karba-karba a gaban mai sanya idanu na Majalisar Dinkin Duniya Martin Kobler gami da jami'an diplomasiya a kasar Moroko.

An dai samun nasarar kulla yarjejeniyar ce a tsakanin bangarorin biyu na kasar Libiya da ta sha fama da zub da jani bisa sanya hannun Majalisar Dinkin Duniya