1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaLibiya

Hadin kai a kokarin warware rikicin Libiya

Kersten Knipp ZUD/ZMA
April 23, 2026

A karon farko cikin shekaru, ana ganin alamun kusantar juna tsakanin bangarorin da ke gwabza fada a rikicin kasar a Libya.

https://p.dw.com/p/5CiLO
Libyen Sirte 2026 | Übung Flintlock 2026 | US- & libysche Spezialeinheiten trainieren gemeinsam
Hoto: Special Operations Command Africa

Hakan ta samu ne a yayin da sojoji daga bangarorin biyun suka hadu a wani atisayen soja na kasa da kasa karkashin jagorancin Amurka. Sai dai masana na gargadin cewa wannan na iya zama mataki na farko ne kawai a kokarin mayar da kasar cikin hayyacinta.

A karkashin atisayen soja da aka yi wa lakabi da "Flintlock” da Amurka ke jagoranta, sojoji daga kasashe kusan 30 na gudanar da atisaye a Libya da Cote d'Ivoire, inda suke samun horo kan yaki da ta'addanci da kuma hadin gwiwa a tsakanin kasashe.

Abin da ya ja hankali a wannan karon shi ne yadda a karon farko aka samu wakilci daga bangarori biyu masu yaki da juna a Libiya, matakin da masana ke gani a matsayin wata alama ta kusantar juna. Masaniyar harkokin siyasa Hager Ali da ke aiki a cibiyar GIGA a birnin Hamburg na Jamus ta ce atisayen ya zama wata mahada ta sada zumunci a tsakanin masu zaman doya da manja.

Besuch in Russland | Libyen General Khalifa Haftar
Hoto: LNA/AFP


"Abin da ya bambanta a wannan karon shi ne an gudanar da atisayen a Libya, kuma a karon farko akwai mahalarta daga bangarorin gabas da yamma na kasar. Wannan na daga cikin kokarin hada rundunonin sojojin kasar wuri guda."

Libiya dai na ci gaba da fuskantar rarrabuwar kawuna tun bayan hambarar da gwamnatin Muammar Gaddafi, inda kasar ke karkashin gwamnatoci biyu da kuma kungiyoyin mayakan sa kai. Masana na cewa duk da wannan kusantar juna da bangaorin da ke yakin suka yi a atisayen Amurka, har yanzu kasar ba ta da cikakken tsarin gwamnati mai aiki yadda ya kamata, domin iko na hannun bangarori daban-daban. Sai dai atisayen ba wai Libiya kadai ya shafa ba, a cewar Hager Ali

"Yaki da ta'addanci na daya daga cikin manyan manufofi, musamman a yankin Sahel. Haka kuma akwai damuwa kan karuwar bazuwar makamai sakamakon yakin Sudan, da kuma tasirin kasar Rasha a yankin."

Rahotanni sun nuna cewa Libya na kara zama wata cibiyar fafatawa tsakanin manyan kasashen duniya, musamman saboda albarkatun man fetur da kuma muhimmancin matsayinta a taswirar duniya. A wani bangare kuma, an samu wani ci-gaba na tattalin arziki, inda aka amince da kasafin kudin kasa guda daya a karon farko cikin shekaru masu yawa. Sai dai masana na ganin hakan ma na da nasaba da kokarin rage karfin wasu fitattun mutane masu iko kamar Khalifa Haftar. Hager Ali ta kara da cewa:

Libyen | Besuch russischer Verteidigungsminister Yunus-bek Yevkurov
Hoto: Media office of Khalifa Haftar/AFP


"Hada kasafin kudin kasa wata hanya ce ta rage tasirin tattalin arziki da karfin iko daga wasu bangarori, musamman wadanda ke cin gajiyar rarrabuwar kawuna a kasar."

Duk da haka, masu sharhi na gargadin cewa wadannan matakai ba za su wadatar ba idan har ba a warware manyan matsalolin siyasa da tattalin arziki ba. Wasu na ganin cewa rarrabuwar kawuna a Libya na amfanar wasu masu kumbar susa, domin hakan na ba su damar ci gaba da rike albarkatu da tasiri ba tare da jama'a sun fargaba ba. Saboda haka, duk da alamun hadin kai da ake gani a yanzu, masana na cewa har yanzu akwai sauran rina a kaba kafin a samu cikakkiyar gwamnati mai hadin kai a Libiya.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani