1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojan Amurka za su yi bankwana da Nijar

Gazali Abdou Tasawa
March 28, 2024

A Nijar gwamnatin Amirka ta sanar da amincewa da umurnin hukumomin mulkin sojan kasar na kwashe sojojinsu daga Nijar, bayan katse yarjejeniyar tsaron da ta hada kasashen biyu.

https://p.dw.com/p/4eDl9
Sojojin Amurka na aikin bayar da horo a yankin Agadez na jamhuriyar Nijar
Sojojin Amurka na aikin bayar da horo a yankin Agadez na jamhuriyar Nijar Hoto: Alex Fox Echols Iii/Planetpix/Planet Pix via ZUMA Wire/picture alliance

A wata ganawa ta musamman da jakadar Amirka a Nijar Mme Kathleen Fitzgibbon ta yi da ministan cikin gidan kasar Nijar Janar Mohamed Toumba a ofishinsa ta sanar mashi da cewa, gwamnatin Amirkar na ba da kai bori ya hau game da bukatar hukumomin mulkin sojan kasar Nijar na ganin sun kwashe sojojinsu dubu da 100  da ke girke a arewacin Nijar domin mutunta matakin katse yarjejeniyar tsaron da ta hada kasashen biyu da Nijar din ta yi a cikin watan Maris na wannan shekara.

Karin Bayani: Shugaba Tchiani ya yi magana da Putin

A  jakadar Amirkar a Nijar ta ce duk da katse yarjejeniyar tsaron da ta hada kasahen biyu, Amirka a shirye take ta ci gaba da tallafa wa Nijar a karkashin hukumar raya kasashe ta Amirka ta USAID.

Kudi sama da miliyan 250 na Dalar Amirka ne gwamnatin Amirka ta zuba domin gina babbar cibiyar sojojin Amirkar da ke a Jihar Agadez, kana Amirkar za ta fice ta bar wannan sansanin soji nata ne a daidai loakcin da zaman arba tsakanin kishiyarta ta Rasha da Nijar ke kara armashi.

Karin Bayani: Bude iyakar Nijar da Najeriya, farin cikin 'yan kasuwa

Yanzu ‘yan kasa sun zura ido su ga ko matakin korar sojojin Amirka ba zai shafi harkokin diplomasiyyar kasashen biyu ba a nan gaba kamar yadda ta kasance da Faransa a baya,a daidai loakcin da kasar rasha ke ci gaba da baza komarta a kasar ta Nijar da ma sauran kasashen yankin sahel.