1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaSaudiyya

Amurka na daf da dawo da sayar wa Saudiyya da makamai

May 26, 2024

Ga dukkan alamu Saudiyya za ta koma samun makamai daga Amurka, bayan kwashe lokaci na haramcin samun makamai daga kasar ta yamma. Saudiyyar dai na fama da zarge-zargen take hakki.

https://p.dw.com/p/4gIMp
Antony Blinken da Mohammad Bin Salman na Saudiyya
Antony Blinken da Mohammad Bin Salman na SaudiyyaHoto: BANDAR AL-JALOUD/Saudi Royal Palace/AFP

Akwai yiwuwar Amurka za ta iya janye matakin haramcin sayar wa Saudiyya da manyan makaman yaki cikin 'yan makonnin da ke tafe, kamar yadda jaridar Financial Times ta ruwaito a yau Lahadi.

A cewar jaridar Amurkar ta riga da ta sanar wa da Saudiyya batun janye dokar haramcin, a cewar wata majiya mai tushe mai cikakkiyar masaniya kan lamarin.

Jim kadan bayan kama aiki ne dai a shekara ta 2021, Shugaba Joe Biden ya tsaurara matakai kan musamman hare-haren Saudiyya a kan mayakan Houthi a Yemen, abin da ya haddasa mace-macen fararen hula.

Akwai ma batun zargin da Saudiyyar ke fuskanta kan take hakkin dan Adam, musamman na kisan dan jaridar nan Jamal Khashoggi a shekara ta 2018.

Saudiyya dai babbar abokiyar cinikin makamai ce a duniya musamman ma ga kasar Amurka.