Amurka da Koriya sun kammala taron su a Berlin | Labarai | DW | 18.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amurka da Koriya sun kammala taron su a Berlin

A yau ne aka kammala tattaunawar bangarori biyu na yini uku tsakanin wakilan Amurka dana Koriya ta Arewa a birnin Berlin din tarayyar Jamus.Duk da kalamansa na farko adangane da alamun samun nasarar tattaunawar tasu,mataimakin sakatariyar harkokin wajen Amurka Christopher Hill ya bar birnin na Berlin ayau,akan hanyarsa zuwa yankin Asia,ba tare da cewa komai akarshen wannan ganawa ta yini uku.A kokarinsa na ganin cewa ya dakatar da shirin nuclearn Koriya ta Arewa,komitin Sulhun Mdd ya kakabawa pyangyong takunkumin sayar mata da wasu muhimman kayayyaki da ababan da suka danganci kayayyakin soji.A yau din nedai Mr Hill ya bayyana fatan cewa,zaa koma teburin tattaunawa tsakanin bangarorin nan shida akan rikicin Nuclearn koriya ta Arewan.