Amirka za ta rage dakarun sojinta daga Jamus | Labarai | DW | 16.06.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka za ta rage dakarun sojinta daga Jamus

Ministan harkokin wajen kasar Jamus Heiko Maas, zai kai wata yar gajeriyar ziyarar domin ganawa da takwaransa na Poland a birnin Warsaw domin tattauna batun Amirka na janye sojinta daga kasashen.

Ziyara da ke zuwa biyo bayan shirin shugaban Amirka Donald Trump ya fara batun janye dakarun sojin kasarsa da ke jibge a kasashen na  Jamus da Poland.

Akwai sojojin Amurka kimanin dubu talatin da dari biyar, a dadin da ke zama kasa da wadanda ke girke a kasar lokacin yakin cacar baka 

Mr Trump na zargin Jamus da rashin biyan isassun kudin kare kanta. Inda ya ce idan aka rage yawansu zuwa dubu 25 zai ga ko za su daidaita.

Ita kuma a nata bangaren kasar Poland na kokarin kara yawan dakarun Amirka ne a kasar ta wanda ta ce hakan na da matukar muhimmanci ga harkokin tsaronta.