Amirka za ta kara yawan dakarunta a Jamus
April 15, 2021Talla
Lamarin kara yawan dakarun ya yi hannun riga da kudurin tsohon shugaban kasar Donald Trump da ya kuduri zabge yawan dakarun. Sanarwar hakan ta biyo bayan ganawar da sakataren ya yi da ministar harkokin tsaron Jamus Annegret Kramp-Karrenbauer a birnin Birlin, kuma a dai dai lokacin da kasar ta Amirka ta bayar da sanarwar janyen dakarunta a Afghanistan nan da 11 ga watan Satumbar wannan shekarar. Matakin da Amirkar ta dauka na kara yawan dakarunta a Jamus, wata hanya ce ta sake farfadowa da kyakyawar alaka tsakanin kasashen biyu da ma sauran kasashe mambobin kungiyar tsaro ta NATO.