Amirka ta gurfanar da Volkswagen | Labarai | DW | 04.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka ta gurfanar da Volkswagen

Sashin kula da harkokin shari’a a kasar ta Amirka a hukumance ya gurfanar da kamfanin kirar motoci na Jamus mai suna Volkswagen saboda illata muhalli.

VW Auspuff Abgasskandal Diesel Benzin Öl Wirtschaft

Alamar motocin Volkswagen VW

A ranar Litinin din nan mahukunta a Amirka sun bayyana a hukumance cewa sun gurfanar da kamfanin Volkswagen saboda zamba me alaka da nau'urar da ke bada bayanai marasa inganci a injinin motocin kamfanin a kasar Amirka.

A cewar mahukuntan kasar ta Amirka dai sun sami wannan na'ura da ba ta bada bayanai na gaskiya a kusan motocin kamfanin 600,000 wadanda aka sayar da su a Amirka kadai. Za dai a iya cin tarar kamfanin Dala miliyan dubu ashirin kan wannan zamba.