Bayanai sun nuna cewa tun da daɗewa Amirka ke naɗan bayanan manyan shugabanin ƙasashe ba tare da an ɗago ta ba.
Tun bayan da tsohon jami'in leƙen asirin Amirkan nan Edward Snowden ya kwarmato bayanan dake nuna cewa Amirka na satan bayanai, ƙasashe da dama sun yi iƙirarin ɗaukar matakai kanta kuma wannan na cigaba da janyo tsamin dangantaka tsakaninta da ƙawayenta.