1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Siyasa tsakanin Amirka da ƙawayenta

Usman ShehuOctober 30, 2013

Fallasa ayyukan jami'an leƙen asirin Amirka da ya kai ga sauraron maganar shugabanni da ake yi ta waya, a yanzu ya tada mahawara mai zafi

https://p.dw.com/p/1A988
CANNES, FRANCE - NOVEMBER 04: In this photo provided by the German Government Press Office, German Chancellor Angela Merkel and US President Barack Obama talk before the meeting on the second day of the G20 Summit on November 4, 2011 in Cannes, France. World's top economic leaders are attending the G20 summit in Cannes on November 3rd and 4th, and are expected to debate current issues surrounding the global financial system in the hope of fending off a global recession and finding an answer to the Eurozone crisis. (Photo by Guido Bergmann/Pool via Getty Images)
Merkel da ObamaHoto: Getty Images

Batun sauraron bayanai na wayar salular shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel dai, kusan ya kasance wa Amirkawa an tada su ne daga barci. Domin kuwa yanzu batun ya mamaye kafafen yaɗa labaran Amirka, inda wasu Amirkawan ke ta zanga-zangar neman a taƙaita bayanen da ake sauraro.

Bullowar wannan batun sauraro bayanen, shi ne ya sa ƙungiyar Tarayyar Turai, ta aika da wata tawoga ta musamman zuwa ƙasar ta Amirka, domin ganawa da hukumomi a Washington. Viviane Reding kwamishiniyar shari'a ta EU, wadda ke cikin tawogar ta faɗawa DW cewa.

"An fargar da Amirkawa. Yanzu ya rataya kanmu shugabanni, mu tabbatar da cewa an kuma ɗauki matakan siyasa da za su biyo baya"

A yanzu haka dai Amirkawan na masu cewa, matakan da jami'an leƙin asiri na NSA da kuma Shugaba Obama suka ɗauka sun yi nisa, kan sirri da kuma 'yancin 'yan ƙasar.

Immigrants protest in favor of comprehensive immigration reform while on the West side of Capitol Hill in Washington, April 10, 2013. REUTERS/Larry Downing (UNITED STATES - Tags: POLITICS CIVIL UNREST SOCIETY IMMIGRATION) // eingestellt von se
Amirkawa ke zanga-zanga gaban majalisar dokokiHoto: Reuters

"Sun faɗa min cewa koda a ƙarshen wannan makon, mahawara kan batun, yanzu ya ɗauki zafi a mazaɓun 'yan majalisar dokokin Amirka. Mutane na cewa ba su fahimci dalilin aikata hakan da ake yi ba"

Bayan matsazin lamba daga ciki da wajen Amirka, bisa batun sauraron bayanen jama'a dai, rahotonni suka ce hakan ya tilasta wa gwamnatin Amirka duba yiwuwar sauya dokokin da ake amfani da su. To sai dai abin da ba a sani ba shi ne, wane ɓangaren dokar ne za a yi wa kwaskwarima, abin da kuma koda a hirarsa da kafafen yaɗa labarai, Shugaba Obama bai fayyace ba. Sai dai Rudy deLeon ɗan majalisar dokokin Amirka, wanda tun bayan harin 11 ga watan Satumba na shekara ta 2001, yake tsakiyar al'amuran da suka shafi dokokin yaƙi da ta'addanci, ya yi ƙarin haske.

"Da farko dai ina jin bai kamata ka tinkari ƙawayenka ba. Bai kamata ka tuhumi abokanenka, waɗanda suke shugabannin ƙasashe ba. Ina ganin waɗannan su ne sauye-sauye da fadar White House ke magana akai. Na biyu kuma, ina jin dole a tantance waɗanne irin bayanai ne, ya kamata hukumar leƙen asiri ta saurara. Dole mu samu kekkewan tsari kan 'yancin sirri jama'a"

President Barack Obama, flanked by European Council President Herman Van Rompuy, left, and European Commission President Jose Manuel Barroso speaks to the media, Monday, Nov. 28, 2011, in the Roosevelt Room of the White House Washington. (Foto:Haraz N. Ghanbari/AP/dapd)
Obama na ganawa da shugabannin EUHoto: dapd

Yayin da kwamitin majalisar dokokin Amirka da ke kula da leƙen asiri ke nuna buƙatar kare lafiyar Amirkawa, amma su ma kansu fallasar batun sauraron wayoyin mutane kamar shugabar gwamnatin Jamus da wasu shugabannin Turai, tabbas wata babbar mahawara ce, da ba za ta tsaya a kafafen yaɗa labarai kawai ba. Dole ta kasance a aikace, inji Larry Korb dan majalisar dokokin Amirka.

"Ina ganin za mu samu dokokin da za su shata iyakar abin da jami'an leƙen asiri za su iya yi a cikin gida da kuma a wajen ƙasarmu. Kamar misalin yadda lamarin yake a hukumar leƙen asiri ta CIA, idan tana son kai farmaki a wata ƙasa, to shugaban ƙasa yakan sanarwa kwamitin majalisar dokoki. Ina jin dole sai an yi hakan."

Bayan ziyarar da jami'an Tarayyar Turai suka kai, a yanzu batun zai rataya ne kan hukumomi da kuma jami'an leƙen asirinn ƙasashen na Turai, domin su duba yadda za su bullo wa matakan magance lamarin. Ta yadda za a kauce wa ɓaraka a tsakanin ƙawaye na ƙut-da-ƙut.

Mawallafa: Gero Schließ / Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu