Amirka da Turai na tir da rikicin Libiya
August 26, 2014Talla
Kasashen Yamma na yin Allah wadai da tashin hankalin da ke faruwa a kasar Libiya. Fada tsakanin kungiyoyi da kabilu sai karuwa yake yi a kasar, tun bayan da aka kifar da gwamnatin Gaddafi a shekara ta 2011. Wata sanarwar da ta samu sa hannun kasashen Faransa, Italiya, Birtaniya, Amirka da Jamus, duk sun yi kira da a samu tsagaita wuta nan take. Sun kuma yi gargadin cewa duk wata katsalanda daga waje, zai kara dagula al'amura, kana ya kara kawo koma baya ga samar da demokradiyya a kasar ta Libiya. A jiya Litinin ne dai, 'yan majalisar dokoki suka koma aiki, inda za su rusa gwamnatin wucin gadi da aka kafa watanni biyu da suka gabata.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Umaru Aliyu