Amirka da China sun amince da rage gurbata yanayi | Labarai | DW | 03.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Amirka da China sun amince da rage gurbata yanayi

Amirka da China sun amince da yarjejeniyar rage iska mai gurbata yanayi.

Shugaba Barack Obama na Amirka da Shugaba Xi Jinping na kasar China sun amince da fara aiki da yarjejeniyar birnin Paris na kasar Faransa kan rage fitar da iska mai gurbata yanayi. A wannan Asabar shugabannin kasashen biyu da suke kan gaba wajen fitar da iskar mai gurbata sararin samaniya suka tabbatar da haka yayin da China ta fara tarbar shugabannin kasashen masu kafin arziki na duniya karkashin kungiyar G20.

Matakin kasashen na Amirka da China ya tabbatar da ceqa zuwa karshen wannan shekara za a fara aiki da yarjejeniyar ta birnin Paris, da za ta taimaka wajen rage dumamar yanayin duniya.

Tuni babban jami'in Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya nuna jin dadi da wannan matakin na kasashen Amirka da China.