1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka: Ci gaba da barazanar kai hari Siriya

Salissou Boukari
April 11, 2018

Shugaban Amirka Donald Trump ya sanar da Rasha cewa, za su kai hare-hare a kowanne lokaci kan muradun gwamnatin Siriya. Kalaman na shugaban Amirka na zuwa ne bayan da fadar shugaban Rasha ta Kremlin ta yi kashedi.

https://p.dw.com/p/2vsQZ
President Trump comments on Syria, FBI raid of Michael Cohen's office at White House
Hoto: picture alliance / Newscom

A wani sako da ya wallafa ta shafinsa na Twitter, Shugaba Trump na Amirka ya zargi kasar Rasha da ke zaman babbar mai marawa gwamnatin Bashar Al-Assad na Siriya baya, da laifin kai harin makami mai guba kan 'yan tawaye a birnin Douma na yankin gabashin Ghouta, zargin da Rasha da siriya suka sha musantawa.

 

Rasha dai ta sha alwashin kakkabo duk wani makami mai linzami da za a harba kasar ta Siriya. Sai dai kuma shugaban Amirka ya ce Rashan ta shirya, domin kuwa makami mai linzami sabo fil na nan tafe. Daga nata bangare kasar Turkiya da ke da ruwa da tsaki akan rikicin na Siriya, ta yi kira ga kasashen na Rasha da Amirka da su daina wannan fada da suke da ke zaman fadan kan titi.