Al'ummar Djibouti na zaben shugaban kasa a wannan Juma'a
April 10, 2026
Al'ummar Djibouti na zaben shugaban kasa a wannan Juma'a, wanda ake hasashen shugaba Ismail Omar Guelleh mai shekaru 78, zai lashe, domin zarcewa a wa'adin mulki na shida.
Shekaru 27 ke nan shugaba Ismail Omar Guelleh ya shafe yana mulkar Djibouti, mai mutane miliyan daya, bisa tafarkin kama-karya a kasar mai arzikin gabar ruwa, wadda sojojin kasashe daban-daban na duniya ke da sansanin soji.
Karin bayani:Ministan harkokin wajen Jamus na ziyara a Afirka
Samar da sansanoni ga kasashen Faransa da Amurka da China da Japan har ma da Italiya, ya bai wa Djibouti sukunin cin moriyar makudan kudi da tallafin tsaro da kulawa a fagen siyasar duniya.
Karin bayani: Zaben Yuganda ya dauki hankulan jaridun Jamus
To sai dai hakan bai amfanar da al'ummar kasar ba, wadda kashi 70 cikin 100 na matasanta ke fama da rashin aikin yi, baya ga dimbin bashi da ya yi wa kasar katutu da dai sauran matsaloli, kamar yadda kungiyoyin kare hakkin dan adam a kasar ke kokawa a kai.