Alamun cutar Ebola | Zamantakewa | DW | 14.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Alamun cutar Ebola

Cutar kan bayyana kawanaki 2 zuwa 21 bayan shigarta jikin bil Adama.

Alamun kamuwa da cutar Ebola kan bayyana ne tsakanin kawanaki 2 zuwa 21 bayan shigar cutar jikin bil Adama. A wasu lokuta alamun kan bayyana tsakanin kwanaki 8 zuwa 10 bayan an kamu kuma suna kama ne da alamun kamuwa da zazzabin cizon sauro (malaria) ko mura. Alamun dai sun hada da:

 Zazzabi

 Kumallo

 Gudawa

 Ciwon makogaro

 Ciwon kai

 Ciwon jiki

 Ciwon ciki

 Kasala

 Rashin son cin abinci

Ba lallai ne dukkan wadannan alamun su bayyana ba, wasu suna iya ganin alamu biyu kacal, misali jini na iya fitowa daga kafofin wadansu daga yikin bangarorin jikin mutun, wadanda suka hada da hanci, da baki da kuma al'aura

Sauti da bidiyo akan labarin