Agadez: Matakan kawo karshen sana′ar safarar bakin haure | Hangen Dala ba shiga birnin ba! | DW | 02.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Hangen Dala

Agadez: Matakan kawo karshen sana'ar safarar bakin haure

Tafiyar hawainiya wajen cika alkawuran da aka yi wa matasa masu safarar bakin haure na samar musu da aikin yi na halan.

A cikin watan Oktobar shekarar da ta gabata aka yi wani babban taro da ya hada kungiyoyin fararen hula da hukumomin jihar Agadez da ma masu hannu da shuni kan batun hana safarar bakin haure, inda aka dauki alkawura da dama da suka hada da sama wa matasa ayyukan yi da za su maye gurbin sana'ar safarar ta bakin haure. Sai dai har yanzu shiru kake ji babu wani labari mai gamsarwa da ya shafi alkawuran. Bachir Ama dan Caga ne na bakin haure kira ya yi ga hukumomin Nijar kamar haka:

"Tun lokacin da muka dauki alkawari mun bar wannan aiki, shi yasa yanzu kira muke yi ga shugabannin da su yi mana kokari alkawuran nan da suka dauka to su yi da gaggawa cikin shekarar nan ta 2017."

shi kuma Abdrahmane Ousmane Kutata shugaban majalisar matassa a jihar Agadez cewa ya yi 'yan Afirka da kansu ya kamata su tashi don kawo maganin matsalar ta hanyar kirkiro da ayyuka ga matasa da kamanta gaskiya na shugabanin Afirka, amma ba EU ba.

"Tarayyar Turai ba za ta taba son ci-gaban Afirka ba har abada tun da ba ta so shia shekarun baya. Saboda haka muke ganin ya kamata mu yi nazari kwarai kan wannan matsala ta matasa da ke tafiya kuma suke mutuwa cikin hamada ko cikin ruwa. Ya kamata mu 'yan Afirka mun san matakan da za mu dauka don mu bunkasa kasashenmu."

Kaura na da asali tun shekaru aru-aru

Sai dai kungiyoyin fararen hula na Agadez na ganin wannan batu na hana safarar bakin haure batu ne mai wuyar aikatawa, inji Lawali Oudoun na kungiyar farar hula a Agadez.

"Wannan kaura cikin jininmu take. Tun da iyayenmu da kakanninmu cikin sarka aka daukesu aka kai su Turai ba tare da bisa ko fasfo ba. Ba a ce kaura ba ta da kyau tun a lokacin ba. Don sun ga amfaninta. Sun gina Turai, sun gina Amirka, sun gina kasashen duniya gaba daya." 

To ko mai hukumomin jiha ke cewa dangane da batun na alkawuran da suka dauka wa matasan masu safarar bakin hauren Ahmed Koussa shi ne mataimaki na biyu na magajin gari cewa yayi.

"Abubuwa biyu za su yi mana magani, na daya shi ne abokan huldarmu su bada kudade a basu su tallafa wa aikace-aikacen da suke yi. Na biyu kuma mu za mu saka ido kan ayyukan na."

Sauti da bidiyo akan labarin