Afirka: Matsalar tsaro a shekara mai karewa | BATUTUWA | DW | 29.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Afirka: Matsalar tsaro a shekara mai karewa

A Arewa maso gabashin Najeriya matsalar tsaro ta kasance mafi jan hankali a shekara ta 2017 bayan ikirarin da rundunar sojojin kasar su ka yi na kashe kaifin kungiyar Boko Haram, ta yadda ba su da sauran tasiri.

Nigeria Militär Präsident Muhammadu Buhari (NPR)

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da tawagarsa yayin ziyara ga sojoji a Maiduguri

Tun bayan da sojojin tarayyar Najeriya suka yi shelar kwace babban sansanin da aka ce na mayakan Boko Haram ne a dajin Sambisa da ke jihar Borno a watan Disambar shekara ta 2016, yawancin al'ummar shiyyar Arewa maso gabashin Najeriyar da ma sauran sassan kasar suka fara kyautata zaton za a samu saukin matsalar tsaro da ta addabi yankin kana ta gurgunta harkokin rayuwa musamman a Jihohin Borno da Yobe. Sai dai sabanin haka mayakan na Boko Haram sun kai munanan hare-hare a kauyuka da dama a jihohin Borno da Yobe inda suka hallaka jami'an tsaro da kuma fararen hula. Haka kuma Kungiyar ta tsananta kai kai hare-haren kunar bakin wake da suka hallaka mutane da dama a jihohin Borno da Yobe da Adamawa, inda kusan kullum sai jami'an tsaro sun dakile yunkurin kai hare-hare da mayakan kungiyar ke yi Maiduguri.

Nigeria Anschlag auf Moschee in Mubi (picture-alliance/AP Photo)

Harin ta'addanci a babban masallacin Mubi da ke jihar Adamawa a Najeriya

Hare-hare masu yawa tare da sace mutane

Hari na farko da kungiyar ta kai a wannan shekarar shi ne na ranar bakwai ga watan Junairu inda ta hallaka sojoji guda biyar a Buni Yadi da ke jihar Yobe. Tun daga ranar ba a kare shafe wata guda ba tare da kungiyar ta kai hare-hare ba har zuwa karshen shekarar. Hakan dai ya sa al'ummar yankin bayyana mabanbantan ra'ayoyi kan lamarin tsaron a shekarar mai karewa. A cikin wannan shekara mai karewa kungiyar ta Boko Haram ta kai hare-hare masu yawa ciki da wajen jami'ar Maiduguri, inda suka hallaka wani shehin malami mai suna Farfesa Aliyu Mani da kuma wasu dalibai da masu tsaron jami'ar. Kungiyar ta kuma kara sace mutane tare da yin garkuwa da su. Mafi fice a cikin wadan aka kame a wannan shekarar ta 2017 shi ne matan 'yan sanda da mayakan suka yi wa kwanton bauna a hanyar Damboa zuwa Maiduguri da kuma harin da aka kai wa ma'aikatan kamfanin mai na kasa da ke aikin binciken albarkatun man futur a bakin gabar tabkin Chadi, inda suka yi awon gaba da wasu malamai da ma'aikatan jami'ar Maiduguri.

Nigeria Selbstmordattentäter greifen Hilfs-Zentrum in Maiduguri an (Getty Images/AFP/Stringer)

Jami'an tsaro na tan-tance gawarwaki bayan harin ta'addanci a Maiduguri

Shakku kan ikirarin samun nasarar sojoji

Yayin da ake shakkun nasarorin da sojojin suka cimma a wannan shekarar, kakakin rundunar sojojin ta kasa a Najeriya Birgediya Janar Sani Usman Kuka Sheka ya kare jami'an tsaron. Yayin da shekarar ke karewa ne kuma rundunar sojojin Najeriyar ta sauya jagorancin rundunar da ke yaki da Boko Haram mai lakabin "Operation Lafiya Dole", inda aka bai Manjo Janar Rogers Nicolas wanda ya nemi hadin kan al'umma don magance matsalar tsaro. Al'ummar yankin na fatan samun saukin wannan matsala ta tsaro a shekara ta 2018 mai kamawa.

Sauti da bidiyo akan labarin