Afirka: An dage dokar hana zirga-zirga | Zamantakewa | DW | 02.07.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Afirka: An dage dokar hana zirga-zirga

A kasashe da dama na Afirka, an dage dokar hana ko takaita zirga-zirga da aka sanya sakamakon bullar annobar cutar coronavirus da ta addabi duniya.

Karikatur Nigeria locked some cities because of Coronavirus

Jiragen sama za su fara jigilar fasinja a cikin gida, bayan an dakatar saboda coronavirus

An dai samu koma bayan a fanonni da dama musamman ma na tattalin arziki da kasuwanci da kuma ilimi, sakamakon barkewar annobar cutar coronavirus da ta addabi duniya. Zirga-zirgar jiragen sama ma ta samu nakasu, kasancewar an sanya dokar ba shiga ba fita a kasashen da wannan cuta tai musu kaka gida. Sai dai tuni aka fara dage dokar hana shige da ficen a kasashe da dama cikin kuwa har da nahiyar Afirka.

A Najeriya ma dai an dauki irin wannan mataki, sai dai kuma za a fara ne da jigilar fasinjoji a cikin gida, inda jiragen za su fara jigilar a ranar Larabar makon gobe, takwas ga wannan wata na Yuli da muke ciki a Abuja da Lagos. Yayin da kuma za a bude filayen jiragen sama na Kano da Fatakwal da Owerri da kuma Maiduguri a ranar 11 ga watan na Yuli da muke ciki. Ministan sufurin jiragen sama na kasar Hadi Sirika ne ya sanar da hakan a shafinsa na twitter, inda ya ce za a bude sauran filayen jiragen saman kasar domin jigilar fasinja a cikin gida a ranar 15 ga watan na Yuli.

Sirika ya kara da cewa za a sanar da ranar da za a bude filayen jiragen saman domin fara jigilar fasinjoji zuwa ko kuma daga kasashen ketare. Laberiya ce dai kasa ta farko a yammacin Afrika da ta bude filayen jiragen samanta, domin fara jigilar fasinjoji, fannin da shi ne ke kawo mata kaso mafi tsoka na kudin shiga.

DW.COM

Sauti da bidiyo akan labarin