Afirka a Jaridun Jamus: 28.08.2020 | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 28.08.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afirka a Jaridun Jamus: 28.08.2020

Batun samun nasarar fatattakar cutar polio ko shan inna a Afirka, na daga cikin batutuwan da suka dauki hankulan jaridun Jamus na wannan makon.

Nigeria Polio Virus (Getty Images/AFP/P. Utomi Ekpei)

Mutane da dama sun nakasa tun suna yara kanana, sakamakon cutar polio

"An ci nasara a kan polio" taken labarin da jaridar Neue Zürcher Zeitung ta rubuta ke nan dangane da ayyana kawar da cutar polio a Afirka da Hukumar Lafiya taduniya wato WHO ta yi a wannan makon. Najeriya ta kasance kasar Afrika ta karshe da ta sanar da bullar cutar shekaru hudun da suka gabata. Godiya ga gagarumin shirin allurar rigakafi da aka kaddamar a wannan kasa da ta fi kowacce yawan al'umma a wannan nahiya. Wannan nasarar na nuni da cewar, an kama hanyar shawo kan wannan cuta a fadin duniya baki daya.

Kwalliya ta biya kudin sabulu

Yaran da shekarunsu ba su wuce biyar ba ne ke fuskantar barazanar kamu wa da kwayar cutar ta polio, kuma cikin sa'o'i kalilan za ta iya shanye wani bangare na jikinsu har abada. Cutar polio ta kasance barazana har ya zuwa shekarun 1990. Kwayar cutar polio ta nakasa yara dubu 75 a nahiyar Afirka a shekara ta 1996. Tun daga wannan lokaci ne al'ummomin kasa da kasa a karkashin wani shiri na yaki da polio da aka kaddamar a shekara ta 1988 a karkashin jagorancin WHO, ya duka ka'in da na'in wajen yaki da cutar. Shirin ya lakume kudi dalar Amirka biliyan 20, kuma kwalliya ta biya kudin sabulu. Domin a Afghanistan da Pakistan ne kadai ake da Polio a yanzu.

Mali Massenkundgebung in Bamako (picture-alliance/AP Photo)

Al'ummar Mali sun yi murna da juyin mulki

Ita Kuwa jaridar Die Zeit sharhi ta rubuta mai taken "Wannan isasshen dalili ne na yin murna"?. Ta ci gaba da cewar, a lokacin da sojojin Mali suka kifar da mulki a makon da ya gabata, nan take ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas ya bukaci da a koma tafarkin kundin tsarin mulkin kasar. Kamar dai sauran takwarorinsa na wasu kasashe. Majalisar Dinkin Duniya ta yi tir da juyin mulkin, a yayin da kungiyar ECOWAS ko CEDEAO ta kakabawa kasar takunkumi. Dokar kasa da kasa dai ta haramta juyin mulki.

An dade ana ruwa

Yawancin al'ummar kasar ta Mali dai, sun yi mamakin furucin ministan harkokin wajen na Jamus, ganin cewar tuni kasar ta sauka daga aiki da kundin tsarin mulki. Tsawon shekaru kenan da Malin ta tsinci kanta cikin wadi na tsaka-mai-wuya. A kan haka ne Al'ummar Malin suka yi kokarin korar gwamnatin shugaba Ibrahim Boubacar Keita da ake wa lakabi da suna IBK ta hanyar zanga-zanga a kasar baki daya. Gwamanatin Tarayyar Jamus da sauran takwarorinta na Turai sun yi kunnen uwar shegu da halin da kasar ke ciki, duk da cewar rundunar sojojin Jamus ta Bundeswehr na bangaren rundunoni biyu na kasar, guda a karkashin rundunar samar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya yayin da dayar kuma ke cikin rundunar EU, masu aikin bayar da horo ga sojojin Malin.

Murna da juyin mulki?

A yanzu haka Berlin da Brussels da uwa uba Paris, wadda ke jagorantar rundunar hadakar da ke yaki da kungiyoyin masu tayar da kayar baya a yankin Sahel, na cikin takaici. Shin ya ya za su yi da masu kifar da mulki da jama'a ke yabo? Kuma su wane ne muhimman abokansu a tsakanin kasashen yammacin Turai? Assimi Goita, shi ne shugaban kwamitin juyin mulkin da ke kiran kansu"masu ceton al'umma". Kuma ya samu horo a Jamus da Amirka da wasu wuraren.

Südafrika Essenshilfe für Bedürftige in Johannesburg (Getty Images/AFP/M. Longari)

Anobar corona da matsalar karancin abinci a Afirka"Afrika na jin radadin annobar COVID-19 a fakaice" wannan shi ne taken labarin da jaridar Neue Zürcher Zeitung ta wallafa, dangane da halin da ake ciki game da annobar cutar coronavirus a Afirka. Ta ce duk da cewar adadin wadanda suka mutu ba su yi yawa ba, akwai yiwuwar adadin zai karu daga wasu cututtuka. Annobar coronar dai ba ta yi barna a Afrika kamar yadda aka yi fargaba ba.

Cututtuka da karancin abinci 

Sai dai duk da haka annobar coronavirus za ta lakume rayuka a yawancin kasashe masu tasowa, saboda abubuwan da ta janyo. Hukumar Bayar da Tallafin Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewar yawan wadanda ke fama da yunwa zai ninka na yanzu. Kazalika, kimanin mutane miliyan 400 za su fada cikin matsanancin talauci. Baya ga haka kuma, akwai matsalar sauran cututtuka masu yaduwa a yankuna masu zafi kamar zazzabin cizon sauro da makamantansu.

 

Sauti da bidiyo akan labarin