AfD ta karbu a zaben jihohin Jamus | Siyasa | DW | 14.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

AfD ta karbu a zaben jihohin Jamus

Sakamakon zaben da aka gudanar a karshen mako a jihohin Baden Wuttemberg da Rhineland Palatinate da Saxony Anhalt na Jamus, ya nuna cewar jam'iyyar AfD ta samu tagomashi.

Shugabar jam'iyyar AfD Frauke Petry

Shugabar jam'iyyar AfD Frauke Petry

Batutuwan da suka hadar da samar da ababen more rayuwa da bunkasa ilimi da kuma tsaro musamman ma abin da ya dangaci jami'an 'yan sanda na daga cikin abubuwan da suka kasance kan gaba lokacin da ake yakin neman zabe a wadannan jihohi. Sai dai maganar 'yan gudun hijira da sauran bakin haure ta sha gaban wadannan batutuwa, kuma wannan batu na karbar 'yan gudun hijira na daya daga cikin abubuwan da jam'iyyar ta AfD ke adawa da shi lamarin da ake ganin shi ya sanyata samun nasarar da ba a zata ba.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel

Masu fashin bakin siyasa a Jamus dai na kallon wannan zabe da ma irin tagomashin da jam'iyyar AfD da ke kyamar baki ta samu a matsayin zakaran gwajin dafi na farin jinin jam'iyyar CDU ta shugabar gwamnati Angela Merkel. Wannan dai a iya cewar shi ne karon farko a dan tsukin nan da wata kankanuwar jam'iyya ta habaka cikin kankanin lokaci.

Sakamako mai ban mamaki

Sakamakon zaben dai ya bai wa 'yan jam'iyyar ta CDU da ma sauran jam'iyyu kamar SPD da ke da karfi a wadannan jihohi mamakin gaske. Guido Wolf na jam'iyyar CDU a jihar Baden-Wuttemberg na da ra'ayin cewa:

"Ba za mu ce mun gamsu da wannan sakamako ba domin kuwa ba abin da CDU ta zaci za ta samu a Baden-Wuttemberg ba kenan, sai dai da ya ke bakin alkalami ya riga ya bushe ba mu da wani zabi illa mu yi kawance da sauran jam'iyyu a wannan yanayi mai wuyar gaske tunda dai jam'iyyar da ta samu nasara a jihar ba ta da rinjayen da za ta iya jagoranci ita kadai."

Malu Dreyer 'yar takarar jam'iyyar SPD da takawararta ta CDU Julia Klöckner

Malu Dreyer 'yar takarar jam'iyyar SPD da takawararta ta CDU Julia Klöckner

Ita ma dai jam'iyyar SPD wadda kamar jam'iyyar CDU ta Merkel ta fuskanci koma baya a biyu daga cikin jihohi ukun da zabukan suka gudana. Nils Schmid da ke zaman jigo a jam'iyyar ya ce sun ji takaicin halin da suka shiga musamman ma a jihar Baden-Wuttemberg a cewarsa sakamakon ya na da ban takaici domin bisa ga abin da suka gani kawance da suka yi da jam'iyyar Greens da ke rajin kare muhalli bai amfana musu komai ba sai tallafawa 'yan Greens din wajen samun nasara.

Abin farin ciki ga AfD

To yayin da jam'iyyun da suka samu ci baya ke nuna rashin jin dadinsu, a hannu guda jam'iyyar AfD ta ce ita kam kamar sallah ko da dai ta ce ba ta ga alamar za ta yi kawance da wata jam'iyya ba a jihar Rhineland-Palatinate kamar yadda Uwe Junge, dan takarar da jam'iyyar ta tsayar a jihar ke cewa:

"Shiga a dama da mu wajen jan ragamar mulki abu ne da zan ce ba za mu yi duba da irin kalaman da jam'iyyun CDU da SPD suka yi ba. Abin da za mu fi mayar da hankali kai shi ne mu kasance babbar jam'iyyar adawa don ci gaba da yada manufofinmu sai dai za mu iya bada gudumawa ga dukkanin shirin da ya dace da akidojinmu da irin tsarin da muke da shi."

A daura da wannan yanayi da ake ciki, jam'iyyar CSU abokiyar tagwaitakar CDU mai mulki, ta shawarci shugabar gwamnati Angela Merkel da ta sake duba matsayin da ta dauka kan batun karbar 'yan gudun hijira domin a cewar CSU din wannan zabe na johohi ukun da aka yi a karshen mako da irin sakamakon da ta samu ya isa ya kasance mata izina.

Sauti da bidiyo akan labarin