Adduo'i ga sojin Jamus da suka rasu a Mali
July 30, 2017Talla
A yayin taron addu'oin Ministar ta bayyana alhininta kan wannan babban rashi. Sojin Jamus akalla dari daya ne suka halaci taron adduo'in a sansanin sojin kasar da ke birnin Gao a arewacin Mali, Ursula von der Leyen ta jadadda matakin gwamnatin Jamus na tabbatar da zaman lafiya a kasashen Afrika wanda ta ce shi ne ginshikin zaman lafiya a kasashen Turai.
Sojojin na daga cikin rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a Mali wato MINUSMA, suna aikin gudanar da aikin binciken sirri a lokacin hadarin da ya yi sanadiyar rayukansu a ranar Larabar da ta gabata. Kawo yanzu dai ba a tantance musababbin aukuwar hadarin ba.
Ana sa ran Ministar tsaron kasar ta Jamus za ta kai ziyara aiki a Jamhurriyyar Nijar nan gaba.