1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Adawa da ci gaban kyamar Islama a Jamus

December 23, 2014

Jamus na zama kasa mafi karfin tattalin arziki a tsakanin kasashen Turai wacce ta kwatanta baki a matsayin bangare na ci gaban shuhurarta a fagen kasuwanci da ci gaban masana'antu.

https://p.dw.com/p/1E9DZ
Anti-Pegida-Kundgebung in Dresden
Hoto: picture-alliance/dpa/Kay Nietfeld

Wani shahararren dan kasuwa a nan Jamus ya bayyana adawarsa da ci gaban karuwan ayyukan masu gwagwarmayar nuna kyama ga mabiya addinin Islama, abin da ya ce maimaikon haka kasar wacce ta zama mafi karfin tattalin arziki a tsakanin kasashen Turai na bukatar baki ne da zasu yi shuhura a fagen hada-hadar kasuwanci da suke neman mafaka a kasar.

Ulrich Grillo shugaban kungiyar masu manyan masana'antu a kasar ta Jamus ya ce maci a mako-mako da masu nuna adawa da yawaitar mabiya addinin na Islama a kasashen Turai na kungiyar PEGIDA , babu abinda zai haifar sai kawo nakasu da zubar da kimar kasar ta Jamus.

Ya fadawa kamfanin dillancin labaran Jamus na DPA cewa Jamus nada tsohon tarihi na karbar baki kuma za ta ci gaba da zama a haka.

Mista Grillo ya bukaci 'yan siyasa da su tashi tsaye wajen adawa da nuna irin akidun kyamar baki na kungiyar ta PEGIDA.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Umaru Aliyu