Abu Namu: Jaruman fina-finan Hausa na samun karbuwa sosai | Zamantakewa | DW | 05.08.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Abu Namu: Jaruman fina-finan Hausa na samun karbuwa sosai

Sana’ar fina-finan Hausa da wakoki na daga cikin sana'o'in da masu yinsu ke kirga riba, farin jinin jaruman fim ya sanya sun samu karbuwa tsakanin mata da maza musamman ma matasa.

Saurari sauti 09:42

Jihar Kaduna guda ce cikin jihohin da jaruman wasan fim da mawaka suke zaune don gudanar da sana'o'insu na debe wa jama’a kewa da kuma ilmantarwa, lamarin da ya sanya duk macen da tsananin shukin son ganin jaruma ya kamata sai ta tattaro kayanta ta zo ta yi ta ragaita, idan an yi sa'a wasu su dace har su shiga sana'ar a fara damawa da su.

Yanzu haka dai sana’ar fina-finan na Hausa da wakoki na daga cikin sana'o'in da masu yinsu ke kirga riba, farin jinin jaruman fim ya sanya sun samu karbuwa tsakanin mata da maza musamman ma matasa.