A Najeriya ta tabbata an yanka ta tashi tsakanin gwamnati da Boko Haram
November 6, 2014Talla
Tun da farko Mahukuntan Tarayyar Najeriya sun ce sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da Ƙungiyar Boko Haram makwanni kusan biyu da suka gabata. Amma kuma daga bisani suka fito suka ce har yanzu da sauran tafiya. Hakan kuwa na zuwa ne bayan da Ƙungiyar Boko Haram ta ƙwace garin Mubi da ke cikin jihar Adamawa da ke a yankin arewa maso gabshin Najeriya,lamarin da ya saka al'ummar yankin cikin wani mawuyacin hali.