1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A gobe Merkel zata fara ziyarar aiki a Washington

January 3, 2007
https://p.dw.com/p/BuVj
Angela Merkel
Angela MerkelHoto: AP
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel na mai ra´ayin cewa fadada hadin kan tattalin arziki tsakanin KTT da Amirka wani muhimmin abu ne. Merkel ta fadawa jaridar Finacial Times da ake bugawa a Jamus cewa Amirka da kungiyar EU na cikin wata tserereniya mai wahala da kasashen nahiyar Asiya kuma watakila nan gaba zata fuskanci wannan matsala a kasuwannin yankin Latun Amirka. Ta ce saboda haka ya kamata a hada karfi da karfe don cimma bukatun juna. A gobe alhamis shugabar gwamnatin ta Jamus zata fara wata ziyarar aiki a Amirka inda zata gana da shugaba GWB.