Ƙasashen Turai za su sake yin taro kan Girka | Labarai | DW | 21.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ƙasashen Turai za su sake yin taro kan Girka

A gobe Ltinin aka shirya ministocin kuɗi na ƙungiyar za su fara taro kafin na shugabannin da yamma da nufin ceton tattalin arzikin Girkan.

Gwamnatin Girka ta gabatar da tayin shawarwari na sauye-sauyen tattalin arzikin ga Jamus da Faransa da kuma Ƙungiyar Tarrayar Turai. Gabannin taron ƙolli na shugabannin naTurai wanda za a yi a gobe Litinin a Brussel.

Firaministan na Girka Alexis Tsipras wanda ya tattauna da shugabar gwamatin Jamus Angela Merkel ta waya tarho da Francois Hollande na Faransa da kuma Jean Claude Juncker na hukumar Ƙungiyar Tarrayar Turai ya ce shugabannin sun ba shi ƙwarin gwiwa a kan shirin.