Ziyarar Merkel ga kasashen Afurka | Siyasa | DW | 02.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ziyarar Merkel ga kasashen Afurka

A ziyararta ta farko ga kasashen Afurka shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel zata yada zango a Habasha da Afurka ta Kudu da Liberia

Angela Merkel

Angela Merkel

A gobe laraba ne idan Allah Ya kai mu shugabar gwamnatin ta Jamus zata tashi zuwa nahiyar Afurka tare da fara ya da zango a kasar Habasha. A cikin wata hira da aka yi da ita Angela Merkel ta nuna cewar ta lura da samun gagarumin ci gaba a kasashe da dama na nahiyar Afurka, kuma a saboda haka ziyarar tata ta farko ga nahiyar Afurka zata kasance ne ga kasashe masu daukar matakai na canje-canjen manufofinsu, wadanda kuma suka zama abin koyi ga sauran kasashen nahiyar. Ita dai Afurka ta Kudu ita ce ta fi kowace kasa a Afurka kakkarfan tattalin arziki, sannan Habasha kuma ita ce shelkwatar kungiyar tarayyar Afurka, wadda ke fafutukar samar da zaman lafiya da tabbatar da mulkin demokradiyya a wannan nahiya. Ita kuwa Liberiya ta tashi ne haikan domin warkar da tabon yakin basassar da ya addabe ta tsawon shekaru da dama. Shugabar gwamnati Angela Merkel ta sikankance cewar kasa ba zata samu ci gaba ba face a karkashin wani yanayi na zaman lafiya da kuma samar da kafofin da suka dace domin cimma wannan manufa.

Merkel ta ce:”Ko shakka babu abu mafi muhimmanci ga jama’a shi ne fita daga kangin talauci. Amma darasin da muka koya a zamanin baya shi ne ko da an gabatar da shirye-shirye na yaki da talauci sai ka tarar babu nagartattun kafofin da zasu tafiyar da wadannan shirye-shirye ta yadda mutane zasu amfana daga garesu. Muddin aka ci gaba akan haka za a wayi gari kwalliya bata mayar da kudin sabulu ba. Ba za a samu nasara ba a wuraren da ake fama da cin hanci ko almubazzaranci. A takaice kasashen dake girmama hakkin al’ummominsu, su ne kawai zasu cimma nasara mai dorewa a matakansu na yaki da talauci.”

Liberiya, a karkashin shugaba Ellen Johnson Leaf da ATK sune misalai kyawawa da za a iya bayarwa a game da kasashen Afurka da suka tashi tsayin daka wajen bin manufofi na canji da tabbatar da demokradiyya da girmama hakkin jama’a. Wadannan kasashe su ne za a fi mayar da hankalinsu a ma’amallar taimakon raya kasa nan gaba, in ji Merkel. A yayinda ta waiwaya zuwa ga dangantakar kasashen Afurka da China kuma shugabar gwamnatin ta Jamus cewa tayi:

Merkel ta ce:”Muna bin diddigin wannan dangantaka sosai da sosai, saboda damuwar da muka yi cewar ana sayen danyyun kayayyaki daga nahiyar Afurka ba tare da an ba da la’akari da manufar nan ta shugabanci na gari ba. Abu mafi alheri nan gaba shi ne duk wata kwangilar da za a bayar a fito da ita ta yadda za a samu tayi daga bangarori daban-daban. Wannan ita ce hanya mafi adalci a ma’amalla da kasashen Afurka.”