1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ziyara Jose Manuel Barroso a Sudan

October 2, 2006
https://p.dw.com/p/Buhd

Shugaban hukumar zartaswa ta kungiar gamaya turai turai, Jose Manuel Barroso ya kai ziyara gani da ido a ƙasar Sudan.

Barroso da tawagar sa, sun tantana da shugaba Omar El Bashir, a game da halin da ake ciki, a Darfur, da kuma mahimmancin aika dakarun shiga tsakani na Majalisar Dinkin Dunia a wannan yanki.

Saidai Jose Manuel Barroso, bai samu nasara ciwo kan shugaban ƙasar Sudan ba, a game da batun amincewa da karɓar rundunar Majalisar Dinkin Dunia.

Bayan wannan tantanwa Baroso da tawagar sa, sun ziyarci Darfur, yankin da ke fama da tashe tsahen hankulla, a tsawan shekaru 3.

A taron manema labarai da ya kira a birnin Al-fasher na yankin Darfur, Jose manuel Barroso, yayi huruci bayan wannan ziyara.

A ɗaya tawagar, EU ta ziyarci cibiyar ƙungiyar tarayya Afrika, a birnin Addis Ababa, na ƙasar Ethiopia, kuma nan gaba a yau za a gana, tsakanin tawagar ta turai, da shugaban hukumar zartaswa na AU, Alpha Omar Konare.