Zargin ′yan ƙetare da hannu a rikice-rikicen Najeriya | Siyasa | DW | 11.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zargin 'yan ƙetare da hannu a rikice-rikicen Najeriya

Hukumar shige da ficcen Najeriya ta fara tasa ƙeyar baƙin hauren da ke ƙasar inda ta ke zarginsu da hannu a hare-haren da ake kaiwa a sassan ƙasar da dama

Ci gaba da kame baƙin hauren da ake yi a Najeriya bisa dalilai na tabarɓarewar rashin tsaro da ake dangantawa da ta’adanci, abinda ke shan kakkausar suka, ya sanya Comptroller Janar na hukumar kula da shige da ficen Najeriya bayyana dalilan ɗaukan irin wadanan matakai da ya ce ba wai sun saɓawa dokokin ƙudurin ƙungiyar ECOWAS ba ne.

Matsalar rashin tsaron Najeriyar da ta sanya ƙara ƙaimi da ake yi wajen kame ko tasa ƙeyar 'yan ƙasashen ƙetare da ake zargin suna zaune a Najeriyar ne ba bisa kaida ba, Irin waɗannan mutane da akan kira su da baƙin haure kuma ake zargin suna da hannu a hare-haren da ake kaiwa a sassan kasar da dama.

Mohammed Yusuf, der Gründer Nigeria's Boko Haram islamistisch

Mohammed Yusuf,

Zargin muzgunawa mutanen da ake tasa keyar tasu zuwa kasashensu na Afrika bisa dalilai na tsaro ya sanya tambayar Rilwanu Bala Musa Comptroller Janar na hukumar shige da ficcen Najeriyar don jin ko me yasa suke kame na kan mai uwa da wabi a kan irin wadanan mutane da kudurin Ecowas ya basu damar shige da fice a kasar.

‘’Yace ba maganar kame-kame bane magana c eta gaskiya don in ka duba kungiyar tarrayar turai ai suna da iznin shige da fice a kasashen da ke tsakaninsu amma ba’a ce ka shiga kowace kasa ba sai kana da izini, cewa aka yi ka yi ta passport, akalla in baka da wannan ka samu takardar izini. To yanzu abinda muka yi don muna manya shine duk wanda ya shigo ba wanan takardun mukan yi mashi rijista musan cewa danb kasa kaza ne. To dole mu yi ta wannan abin don mu san cewa mutanen da zasu shigo su zauna da mu mutanen kirki ne ba wadanda zasu aikata wani aikin asha ba’’.

Yan akasashen Afrika da dama da ke zaune a a Najeriya dai sun dade da nuna korafi a a kan irin wannan kame da suka ce na muzguna masu ne, tare ma da musanta cewar suna da hannu a kai hare-haren da ake yi a Najeriya. Alhaji Abubakar Khal;id shine shugaban yan Nijar a Najeriya.

‘’Yace Mu yan Nijar mazauna Najeriya abinda muke fuiskanta duk wata wahala da ta taso a kanmu take karewa domin duk bakin da ke zaune a Najeriya zamu dauki kasha sabain ko tamani, amma in ka duba har yanzu ba’a fido dan Nijar a fili an kama shi da bindiga ko bomb a ga takardaunsa a ce an kama shi ba. Sai dai zato ne ake yi mana in an tashi sai far mana ait a kamamu, abin kuma na bamu haushi. In har Najeriya ko Nijar basu son zamanmu a nan to shikena sai a fada mana a fito fili a radio sai mu tattara kayanmu mu koma gida’’.

This image taken from video posted by Boko Haram sympathizers shows the leader of the radical Islamist sect Imam Abubakar Shekau made available Wednesday Jan. 10, 2012. The video of Imam Abubakar Shekau cements his leadership in the sect known as Boko Haram. Analysts and diplomats say the sect has fractured over time, with a splinter group responsible for the majority of the assassinations and bombings carried out in its name. (AP Photo) THE ASSOCIATED PRESS CANNOT INDEPENDENTLY VERIFY THE CONTENT, DATE, LOCATION OR AUTHENTICITY OF THIS MATERIAL

Imam Abubakar Shekau

To sai dai sanin cewa hukumar shige da ficen Najeriyar ce aka daorawa alhakin tsare kan iaykokin kasar, wanda bisa tsari bai kamata a ce an bar bakin da basu da takardun sun kaiga shiga Najeriyar ba. Har ila yau ga Comptroller na hukumar kula da shige da ficen jama’a ta Najeriyar.

"Bari in baka misali da Katsina da kuma tsakanin America da Mexico ai har Katanga aka gina amma ni kuma fa ai bani da Katanga bani da komai kuma Hamada ce duk da haka muna kokari don mu kamanta wannan tsaron kuma dole ne mu ci gaba da yin hakan’’.

Sannu a hankali dai kalubalke na rashin tsaro musamman ma dai kai hare-hare na ta’adanci ya jefa Najeriyar cikin mawuyacin halli abinda masharahanta ke bayyana tsoron tasirin da hakan ke yi ga kudurin na Ecowas da ya dade da kokarin dinke kasashen yankin don bunkasar tattalin arzikinsu.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita: Usman Shehu Usman

Sauti da bidiyo akan labarin