Zargin kisan gilla a yankin arewa maso gabashin Najeriya | Siyasa | DW | 05.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zargin kisan gilla a yankin arewa maso gabashin Najeriya

A rahoton da ta fitar, kungiyar Amnesty International ta zargi sojojin Najeriya da kungiyar Boko Haram da kokari na kare dangi a yankin arewa maso gabashin kasar.

Kungiyar Amnesty dai ta ce tana da shaidu a kasa da ke tabbatar da kokarin cin zarafi da ma kare al'umma a bangaren sojan kasar da su ka yi kisan ba gaira ga fararen hular da basu ji ba balle gani cikin rikicin da ke dada sauyin salo da tada hankali a halin yanzu.

Kama daga hotunan da ke nunin yankan rago, ya zuwa ga harbi da kisan da babu gaira cikin sa dai, Amnesty ta ce daruruwan mutane ne aka hallaka a bangaren sojan da ke ikirarin kawo sauyi da ma kungiyar Boko ta Haram din da ke sauyin salo da ma amfani da yara mata a cikin aikin na ta.

Bello Sabo Abdulkadir dai na zaman sakataren kungiyar dattawan Arewa maso gabashin kasar da tun da farkon fari ta nuna bara'arta ga yadda yakin ke tafiya cikin yankin, mutumin kuma da ke fadin rahoton na kara tabbatar da hasashen yanda sojan kasar ke kara mamaye harkokin tsaro da ma mulkin kasar.

“Yanzu za ka iya cewa kusan sojoji ke mulkin kasar, tun da aka fara wannan abu basu taba cewa sun yarda basuyi dai dai ba, haka kuma gwamnatin bata taba yarda da laifinsu ba, Ana fakewa da abun da ke faruwa a yankin Borno da Yobe da Adamawa, ana cin zarafin mutane, su kuma sojoji ana ba su zarafin yakin da ba su je suka yi a wata kasa ba, suna yi kan al'ummar Najeriya. Idan gaskiya ne wannan fa zai nuna wa gwamnati fa cewar fa duniya fa na sane kuma ko ba dade ko ba jima za'a fito a yi wannan bincike. Kuma idan su ne yau ba su ne gobe ba. Kuma duk mai wannan ya sani fa ba wurin buya ranar da gaskiya ta fito.”

Rundunar sojin Najeriya na ikirarin samun nasara

Nigeria Soldaten Archiv 2013

Sojoji sun ce su na iya kokarinsu

Tabbatar da gaskiya komai dacin ta ko kuma kokari na kare dangi dai, tuni sojan kasar da ke fadin za su kai ga bincike, suka ce a fili take, suna samun nasara a cikin yakin na su duk da jeri na zarge-zargen kungiyoyin kasashen da ke cikin gida da ma waje irin na su Amnesty, a fadar Janar Chris Olukolade dake zaman kakakin rundunar tsaron kasar.

“Abun takaici, amma koma mene ne ba zai karya mana gwiwa ba ga cewar muna da aikin hidima ga kasarmu ta haihuwa da al'ummarta. Tunanin wasu can a waje na zaman daban, muna da imanin cewar nan gaba kadan, kowa zai san gaskiya sakamakon nasarar aikin mu. Sukar ba wai tana da nasaba da rashin nasarar aikin namu bane. Aikin mu na samun nasara ga kokarin kare kasa. 'Yancin da yan ta'adda ke samu kafin dokar ta baci ya koma baya. Abun da kawai suke iya yi yanzu shi ne zagaye sassa daban daban suna jawo fitina kan wadanda ba su ruwa balle tsaki. Muna da imanin cewar wadannan din ma za su ragu a nan gaba kadan”

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Pinado Abdu Waba

Sauti da bidiyo akan labarin