1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tashar makamanshin nukiliyar Ukraine cikin hadari

Abdourahamane Hassane
August 16, 2022

Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine ya gargadi kasashen duniya da su yi hattara su kare afkuwar hatsari a tashar makamashin nukiliya ta Zaporizhzhia.

https://p.dw.com/p/4Fa5Y
Ukraine I Zaporizhzhia I Saporischschja
Hoto: Dmytro Smolyenko/Ukrinform/IMAGO

A cikin wani sakon bidiyo da ya bayyana Zelensky ya ce idan har duniya ba ta nuna karfi da azama ba tun da sauran wuri don kare tashar nukiliyar ba, za a iya fuskantar wani baban bala'i na sulalewar turirin iskan gas mai guba. ''Idan har kasar 'yan ta'adda ta yi gaban kanta ta yi watsi da bukatun kasashen duniya a cikin irin wannan batu, mai muhimmanci, to kam akwai bukatar daukar matakin gaggawa saboda duk wani abin da ya faru a tashar makamashin nukiliyar na iya shafar kasashen Turai .Rasha ta kwace tashar makamashin nukiliyar Zaporizhzhia. bayan ta mamaye kasar Ukraine a cikin wata Maris da ya gabata.Tsawon makonni bangarorin da ke gaba da juna suna zargin juna da kai hari kan tashar makamashin nukiliyar mafi girma a nahiyar Turai,