Zanga-zangar ′yan Shi′a a Najeriya | Siyasa | DW | 14.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zanga-zangar 'yan Shi'a a Najeriya

Dubban mabiya darikar Shi'a da ake kira da kungiyar 'yan uwa Musulmi wadda Sheikh Ibrahim El-Zakzaky na Zaria ke jagoranta sun yi wani gangami ko Muzahara ta lumana a garuruwa da dama a Nigeria.

Dubban 'yan kungiyar maza da mata, dama kanannan yara ne suka yi wata zanga-zanga ta lumana inda suke dauke da hotunan shugaban kungiyar Sheikh Ibrahim El-Zak zaky da kwalaye masu dauke da rubuce-rubuce na la'antar shugaban Nageria Goodluck Jonathan, dangane da yunkurin da suka ce ana yi na kashe shugaban kungiyar wato Sheikh El-Zakzaky, inda suka ce take-taken gwamnatin sun nuna haka.

Sheikh Ibrahim El-Zakzaky dai ya fito karara a yan kwanakin nan, yana kalubalanantar gwamnatin Najeriya wadda ya ce ita ke da alhakin kisan gilla da ake yi wa' yan uwa Musulmi a wannan kasa, inda ya kara da cewa al'amarin Boko Haram gwamnati ce da kanta ke aiwatar da kisan mutane da nufin ba da dama ga Amirka da mukarrabanta su mamaye arewa maso gabashin Najeriya inda aka tabbatar da arzikin man fetur.

Sauti da bidiyo akan labarin