Zanga-zangar rushe gidaje a Legas | Labarai | DW | 16.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zanga-zangar rushe gidaje a Legas

'Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zangar zaman dirshan a jihar Legas Kudu maso Yammacin Najeriya a wannan rana ta Alhamis, bayan da wasu tun a jiya Laraba suka kwana inda suke neman hakkinsu.

Kimanin mutane 600 ne daga yankin Otodo-Gbame a jihar ta Legas ciki har da mata da yara a jiya Laraba suka gudanar da maci zuwa ofishin gwamna, sun dai kasance  daga cikin sama da mutane 30,000 da aka raba su da muhallansu a shekarar bara bayan da mahukuntan wannann birni suka kudiri aniya ta kawar da unguwanni na marasa galihu. Akalla mutane 11 ne dai ake cewa sun mutu wasu 17 sun bace lokacin da manyan motocin katafila suka afka rushe matsugunan inda wasu suka ruga da fadawa cikin ruwa.

A farkon wannan mako dai Kungiyar Amnesty International ta fitar da wani rahoto inda ta ce korar al'ummar da ke sana'ar kamun kifi a yankunan da ke kusa da bakin ruwa ya sabawa doka inda suka bukaci a gudanar da bincike kan gallazawar da ake wa al'ummar.