1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Manoman Indiya na shirin fadada zanga-zangarsu zuwa Delhi

Zainab Mohammed Abubakar
March 4, 2024

Daga ranar Laraba ne dai manona ke shirin tsananta gangamin ta hanyar shiga New Delhi babban birnin kasar cikin bas da jiragen kasa, tare da kara toshe kan iyaka da motocin tarakta.

https://p.dw.com/p/4d8x1
Hoto: Manish Swarup/AP Photo/picture alliance

Dubban manoma ne suka fara tattakin da suka kira"Delhi Chalo" wanda ke nufin "Mu je Delhi" a watan da ya gabata, amma jami'an tsaro suka hanasu isa tun a nisan kilomita 200 daga arewacin babban birnin kasar ta hanyar amfani da hayaki mai sa hawaye da ruwan zafi.

Manoman da ke neman a kara farashin amfanin gonakinsu, sun tsananta zanga-zangar ne bayan gazawar tattaunawar da aka yi ta yi da su.

A ranar Laraba ne dai ake saran manoma daga jihohi daban-daban na Indiya, za su isa New Delhi kamar yadda wani shugaban kungiyar manona, Ramandeep Singh Mann,  ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.