1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Manoman Indiya sun yi rikici da 'yan sanda

Mouhamadou Awal Balarabe
January 26, 2021

Arangama ta barke bayan da manoma suka tarwatsa shingaye 'yan sanda a yayin da suke zanga-zangar nuna kyama ga shirin gwamnatin Indiya na sake fasalin aikin gona.

https://p.dw.com/p/3oRB8
Indien Bauernproteste
Hoto: Imtiyaz Khan/AA/picture alliance

Dubban manoman Indiya sun yi amfani da taraktocinsu wajen tarwatsa shingayen da ‘yan sanda suka kafa a kofar shiga birnin New Delhi don hana su gudanar zanga-zanga. Jami'an na tsaron sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye da kuma sanduna wajen tarwatsa su, amma dai ya zuwa yanzu babu adadin wadanda suka jikkata.

  Su dai manoman sun yi amfani da bikin ranar samun 'yancin kan Indiya wajen ci gaba da nuna adawa da shirin gwamnati na sake fasalin aikin gona. Wasu masu zanga-zangar sun yi nasarar kutsawa kusa da wurin da ake bikin ranar 'yanci, inda Firayiminista Narendra Modi ya shugabanci faretin soja. Wannan ita turjiya mafi muni da gwamnatin ta Indiya ta fuskanta a cikin shekaru shida da ta shafe tana mulki.