Zanga-zangar malaman makaranta a Nijar | Siyasa | DW | 28.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zanga-zangar malaman makaranta a Nijar

Kungiyoyin malaman makaranta sun kira wata zanga-zanga domin nuna damuwa a game da saba alkawari da gwamnatin ta yi a kan biyan bukatun malaman na albashi, sai dai wasu daga cikin malaman ba su amince da yin gangamin ba.

Bayan kwanaki da aka kwashe ana kai ruwa rana tsakanin gwamnatin Nijar da dalibai, a yanzu kuma wata sabuwar ta kuno kai inda malaman makarantar suka sha alwashin kalubalantar gwamnatin a kan batun biyan albashi. Wanda malaman makarantar ke zargin gwamnatin da saba alkawarin da ta yi na biyan su kudaden albashin da suke bin gwamnatin bashi. Sai dai kuma an samu rarrabuwar kawuna a tsakanin malaman, yayin da wasu daga cikin malaman suka yi watsi da kiran da kungiyoyin suka yin na yin gangamin don yin Allah dai da gamnatin. Wannan dai ba shi ne karo na farko da irin haka take faruwa ba a Nijar.

 

Sauti da bidiyo akan labarin