Zaman zullumi a babban birnin Tarayyar Najeriya | Siyasa | DW | 02.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zaman zullumi a babban birnin Tarayyar Najeriya

Kara tabarbarewar da matsalar rashin tsaro ta yi a Abuja ya haifar da yanayi na rashin kwanciyar hankali a zukatan mazaunan birnin da ma yankunansa.

Wannan mummunan hali da birnin Abuja ya samu kansa a ciki da a kullum yanayin tsaron ke kara sukurkucewa tun daga 2010 da aka kai harin bom na farko ya kasance abin da ke zama kalubale ba kawai ga mahukuntan Najeriyar ba har ma da mazauna birnin, musamman a dai lokacin da a karon farko Najeriyar ke shirin karbar bakoncin taron kolin tattalin arziki na duniya.

Domin kuwa Abuja ta kasance mafaka ga mafi yawan marasa karfi da babu shiri suka yi gudun hijira daga jihohin da ke fama da irin wannan matsala ta kai hare-haren bama-bamai da sace jama'a da ma fashi da makami. Kasancewar tudun na tsira da suke hango a yanzu ya zama babu tsira a cikinsa bayan da a makwanni kusan uku bom na biyu ya sake tashi a unguwar Nyanya ta marasa galihu, wuraren da dubban jama'a ke samun mafaka ke zama ya sanya wasu mazauna wadannan yankuna bayyana yadda suke ji da rayuwa a yanzu.

Karuwar ayyukan tarzoma duk da matakan tsaro

Abuja 1. Mai-Rallye

"Za mu yi maganin tarzoma"-inji Jonathan a lokacin jawabin ranar ma'aikata

Shin mene ne zahirin dalilin afkuwar hakan, domin kuwa shingayen binciken ababen hawa da aka daddasa a hanyoyin shiga birnin da ma sintiri da jirgin sama mai saukar ungulu kan yi a sararin samaniyar birnin sun kasa yin tasiri. Wannan ya sanya alakanta matsalar da dalilai na siyasa da tuni manyan jam'iyyun kasar biyu na PDP mai mulki da APC kan zargi juna. Amma ga Alhaji Usman Faruk tsohon gwamnan mulkin soja tsohuwar jihar arewa maso tsakiyar Najeriya a lokacin yakin basasa na mai bayyana cewa.

"Ai wannan matsala ta shekara uku ya bani mamaki domin yakin basasa da muka yi a cikin shekaru uku muka gama, yanzu gashi an shekara uku ana fama da wannan matsala ba alamar cewa za ka kwana uku ba ka ji wani abu ya faru ko ya fashe ba. Sannan a wancan lokaci da muka yi wannan yaki a jihohin arewan nan muna da matasa miliya goma sha biyar, kuma daga ciki rabin miliyan kadai muka yi amfani da su, amma yanzu muna da matasa miliyan arba'in, to ko ba a ba su horaswa ba ne ko ba a yi amfani da su ba ne bamu sani ba."

Duk da nanata tabbacin cewa gwamnati na kan wannan al'amari kuma za ta shawo kansa da shugaban kasar Goodluck Jonathan ya kara nanatawa a lokuta da dama, wanda na baya-baya nan wanda ya yi a ranar ma'aikata yana cewa.

"Za mu ci gaba da aiki tukuru domin tabbatar da tsaro ga al'ummarmu, wadanda suka kai hari a Nyanya tabbas za a hukunta su."

To sai dai bayyana take a fili cewa baya ga jefa al'ummar Abujan cikin hali na tsoro tabarbarewar rashin tsaron da ta zo har Abuja fadar gwamnatin Najeriyar na da mummunar illa ga Najeriyar da al'ummarta.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris

Edita: Mohammad Nasiru Awal

Sauti da bidiyo akan labarin