Zaman dar-dar a Gabas ta Tsakiya | Siyasa | DW | 09.01.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zaman dar-dar a Gabas ta Tsakiya

Kisan da Amirka ta yi wa babban kwamandan Iran Qassem Soleimani a Iraki, da martanin da Iran ta fara mayarwa ta hanyar harba makamai masu linzami kan sansanonin Amirka a Iraki, ya janyo zaman dar-dar a Gabas ta Tsakiya.

Kwanaki biyar bayan da Amirka ta halaka Janar Qassem Soleimani, kasar Iran ta mayar da martani ta hanyar harba wasu makamai masu linzami kimanin 15 kan wasu cibiyoyin sojin Iraki guda biyu wadanda sojojin Amirka ke girke a cikinsu.

Harin dai ya ci karo da martani mabambanta daga shugabannin kasashen duniya, wadanda suka yi kira ga kasashen Amirka da Iran da su bi hanyoyin diflomasiyya don warware rikicin tun bai rikide ya zama yaki ba.

DW.COM