Mabambantan martanin kasashen duniya kan rikicin Amirka da Iran | Siyasa | DW | 08.01.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Mabambantan martanin kasashen duniya kan rikicin Amirka da Iran

Tun bayan harin makamai masu linzami da Iran ta kai a kan wasu sansanonin sojin Amirka a Iraki, shugabannin kasashen duniya ke yi ta mayar da martani mabambanta.

Firaminista Boris Johnson na kasar Birtaniya da ke zama babban amini ga shugaban Amirka Donald Trump, ya dauki tsawon lokaci tun bayan kisan Qassem Solemani kafin ya tofa albarkacin bakinshi kan batun. Hakan dai na nuni da goyon bayansa ga matakin na Amirka. Sai dai bai ya yi saurin yin tir da harin makamai masu linzami da Iran ta kai a kan sansanoni sojin Amira da ke Iraki, inda ya ce Amirka na da 'yancin kare dakarunta a duk inda suke a duniya.

"A ganina al'umma za su yarda da cewa Amirka na da 'yanci da ma damar kare dakarunta da sansanonin da suke ciki. Kasar Iran ta dade tana daure wa mayakan Houthi gindi, tana ba su manyan makamai da suke kai hari a kan fararen hula, tana kuma goya wa 'yan Hizbullah baya, bugu da kari duk abin da Assad ya yi a Siriya da goyon bayan Iran."

Firaministan Pakistani Imran Khan da tuni ya zame kasarsa da duk wata tashin-tashina da ka iya tasowa a yankin, ya jadadda muhimmancin yayafa wa wutar wannan rikici da ke shirin barke ruwa. A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Twitter Mr Khan ya ce zai aika da ministan harkokin kasashen waje zuwa Iran da Saudiyya da ma Amirka don lalubo bakin zaren warware matsalar.

Ita kuwa kungiyar kawancen tsaro ta NATO da ke da sojoji kimamin 500 a Iraki da ke horas da sojojin kasar dabarun yaki da mayakan IS sun fara ficewa daga kasar tun bayan da rikicin ya fara. Sakataren kungiyar ta NATO Jens Stoltenberg ya yi tir da harin da Iran din ta kai a kan sansanonin sojojin na Amirka, kana ya yi kira ga Iran da ta guji shiga cikin wani tashin hankali.

Sakataren kungiyar NATO Jens Stoltenberg ya yi kira ga Iran da ta guji tashin hankali

Sakataren kungiyar NATO Jens Stoltenberg ya yi kira ga Iran da ta guji tashin hankali

Shi kuma ministan harkokin wajen kasar Turkiyya Mevlut Cavusoglu a ranar Alhamis zai kai ziyara Iraki a wani bangare na matakan diplomasiyya da ake dauka a kokarin hana rincibewa rikicin. Wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Turkiyya ta bayar, ta ce ministan ya yi magana da takwaran aikinsa na Iran a wannan Laraba bayan harin rokokin da Iran ta kai a sansanonin biyu a matsayin ramuwar gayya ga kisan da Amirka ta yi wa babban kwamandanta Qassen Soleimani a birnin Bagadaza a makon da ya gabata. Turkiyya ta yi kira da a kwantar da hankali sannan ta nuna damuwa game da sha'anin tsaron yankin.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Italiya ta yi kira ga kawayenta na Turai da su yi aiki don samun maslaha.

Ita kuwa ma'aikatar tsraon kasar Sloveniya cewa ta yi za a kwashe sojojinta gida shida tare da wata tawagar masu ba da horo ta Jamus da ke arewacin Iraki. Ta ce za a yi aikin ne tare da hadin gwiwar aminai na Jamus.

A nata bangaren gwamnatin Siriya ta nuna goyon bayanta ne gaba daya ga Iran, tana mai cewa Tehran na da 'yancin kare kanta daga barazana da kuma hare-hare na Amirka.

Wani dan majalisar kasar Rasha ya yi gargadin cewa duk wani rikici tsakanin Amirka da Iran ka iya kai wa ga yakin makaman nukiliya.

Sauti da bidiyo akan labarin