1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Buhari ya ce yana kan hanyar cika alkawarin kasa

June 12, 2020

Najeriya na yin bikin zagayowar ranar dimukaradiyya wanda a kan bikin shugaba Muhammad Buhari ya ce ya yi nisa a kokarinsa na cika alkawarin da ya dauka a tsakaninsa da al'umma kasar.

https://p.dw.com/p/3dhXl
Nigeria Democracy Day 2019
Hoto: Reuters/A. Sotunde

A wani jawabi na kusan mintuna 40 ga 'yan kasar shugaban kasar Muhammad Buhari ya ce kasar tana kan hanyar nasarar a wurare dabam-dabam kama daga hasken wutar lantarki da kasar ke da bukata ya zuwa harkokin noma da gini na layin dogo. Shugaban kasar ya ce gwamnatinsa na kan hanyar cika daukacin alkawuran da ke tsakaninta da al'umma kasar. Ga shi kansa batun tsaron da ya dauki hankali a wannan mako bayan asarar rayuka sama da dari a sassan arewa maso gabas Buharin ya ce rundunar tsaron kasar na samun nasar a kan 'yan ta'addar.

Raunin a kan sha'anin tsaro a Najeriya dab da halin da ake ciki na annobar corona

Nigeria Democracy Day 2019
Hoto: Reuters/A. Sotunde

Kama daga masu adawa ta siyasa ya zuwa ga 'yan sharhi a cikin lamura na kasar dai akwai alamun kasawa musamman ma ga batun tsaro da ke zaman daya a cikin ginshikai guda uku da gwamnatin ta alkawarta ga 'yan kasar. Sanata Umar Tsauri dai na zaman sakataren jam'iyyar PDP mai jagoranta ta adawa a cikin tarrayar Najeriyar da kuma ya ce jawabin bai burge ba musamman halin da kasar ta ce ciki a halin yanzu. Ci da gumin  dalibai cikin annobar Covid 19 ko kuma ci da gumi na 'yan kasar dai ga Auwal Mu'azu da ke sharhi a cikin lamura na kasar duk wani cigaban da ya manta da tsaro to na zaman aikin banza.