Zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasa a Gini | Labarai | DW | 03.07.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasa a Gini

Salihu Dalein Diallo da Alfa Conde za su kara a zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasar Gini

default

Tsohon Firaministan ƙasar Giin Salihu Dalein Diallo, da fitaccen ɗan adawar ƙasar Alfa Conde za su fafata da juna a zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasar Gini, bayan da sakamakon zaɓukan da ƙasar ta gudanar a ranar Lahadin data gabata, wanda hukumar zaɓen ƙasar ta bayyana a jiya Jumma'a, ya gaza samar da wanda ya samu gagarumin rinjaye. 'Yan takarar biyu ne dai suka kasance akan gaba cikin 'yan takara 24n da suka kara a zagaye na farko, yayin zaɓen da masu sanya ido suka kwatanta da cewar shi ne mafi 'yanci da walwalar da ƙasar ta gudanar tun samun 'yancin ta a shekara ta 1958.

Shugaba hukumar zaɓen Gini mai zaman kanta, Ben Seku Sylla ya shaidawa manema labarai cewar sakamakon ya nuna Salihu Diallo ya sami fiye da kashi 39 cikin 100 a yayin da Alfa Konde kuwa ya sami fiye da kashi 20 cikin 100. Alƙalumar da hukumar zaɓen ta fitar, ya kuma nunar da cewar, kashi 77 cikin 100 na waɗanda suka cancanci kaɗa ƙuri'a ne suka fito domin zaɓen, wato mutane miliyan ukku da dubu 3 ne suka fito daga cikin adadin waɗanda aka yiwa rajista miliyan huɗu da dubu 200.

Diallo dai Bafulatani ne, kuma ƙwarare a sha'anin tattalin arziƙi, wanda kuma ya taɓa riƙe muƙamin Firaminista daga shekara ta 2004 zuwa 2006, a yayin da Konde kuwa ya fito daga ƙabilar Malinke, kana ya kasance ɗan adawa ne ga gwamnatocin Gini tun lokacin da ƙasar ta samu 'yanci.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh