1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka: Zabe da makomar Trump

Lateefa Mustapha Ja'afar
November 5, 2018

A karon farko zaben tsakiyar wa'adin mulki na 'yan majalisun dokoki a Amirka da za a gudanar a ranar shida ga wannan wata na Nuwamba da muke ciki, ya dauki hankalin al'ummomin kasa da kasa musamman a nahiyar Turai.

https://p.dw.com/p/37fvo
USA Midterm Wahlen 2018 Stimmauszählung
Zaben tsakiyar wa'adi na 'yan majalisun dokoki a AmirkaHoto: DW/B. Karakas

Daga cikin batutuwan da suka sanya zaben na tsakiyar wa'adi na 'yan majalisun Amirkan ya dauki hankalin duniya musamman ma a kasashen nahiyar Turai dai a kwai batun nan na kasuwanci mara shinge. Jamusawa kamar sauran al'ummomin kasashen nahiyar Turai, na dakon ganin ko Shugaba Donald Trump zai sake takunsa dangane da siyasarsa ta kasashen ketare in har jam'iyyar adawa ta Democrats ta samu nasarar lashe zaben 'yan majalisun na tsakiyar wa'adi. A hannu guda kuma wasu ma na cewa kamata ya yi in har suka samu rinjaye a majalisun dokokin, su gabatar da kudirin tsige Shugaba Trump din. Za dai a sake zaben baki dayan 'Yan Majalisar Wakilai yayin da za a sake zaben kaso daya bisa uku na 'Yan Majalisar Dattawa. A yanzu dai jam'iyyar Republicans ce ke da rinjaye a majalisun biyu.

USA Trump Yellowstone International Airport
Shugaban Amirka Donald TrumpHoto: Reuters/C. Barria

Makomar Trump bayan zaben tsakiyar wa'adi

A bisa tarihin Amirka, zaben tsakiyar wa'adi na 'yan majalisun dokoki na kara karfi ne ga jam'iyyar adawa, abin kuma da a nasa bangaren wani na hannun daman shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da ke zaman kwararre a kan siyasar kasashen Turai daga jam'iyyar CDU Elmar Brok ke ganin a yanzu ma yana iya faruwa, a cewarsa ana iya daidaita wa Trump sawunsa musamman idan jam'iyyar Democrats ta samu rinjaye koda kuwa a Majalaisar Wakilai kadai. Ya kara da cewa hakan zai tilasta wa Trump din gyara dangantakarsa da kasashen ketare. Sai dai a ganin Josef Braml kwararre kan Amirka a cibiyar nazarin manufofin kasashen waje ta Jamus, samun nasarar Democrats ba za ta kawo wani sauyi a yakin kasuwancin tsakanin Turai da Amirka ba, ganin cewa suma 'yan jam'iyyar Democrats sun nuna adawarsu kan kasuwanci mara shinge, shi ma kuma Trump ya bayyana adawarsa kan wannan batu. A cewarsa mafita shi ne kasashen Turai su fara nemarwa kansu mafita, su koyi yin tunani a matsayinsu na ksashen Turai ba tare da dogaro da Amirka ba.

Symbolfoto Verhältnis USA EU
Tsamin dangantakar kasuwanci tsakanin Turai da AmirkaHoto: picture-alliance/K. Ohlenschläger

Dangantakar kasuwancin Turai da Amirka

Tuni kasashen Turai ke cikin firgici dangane da takaddama kan kasuwanci mara shinge tsakaninsu da Amirka. Kwaskwarimar da Donald Trump ke wa fannin kasuwanci a Amirka ya sanya takun saka tsakaninsa da kusan daukacin kasashe masu karfin tattalin arziki na duniya. Kungiyar Tarayyar Turai na yin barazanar kakabawa Amirka gagarumin haraji kan tama da gorar ruwa da take shiga da su kasashen kungiyar, sakamakon barazanar da Trump ke yi na kara yawan kudin fito kan motoci, inda ya ce yana son ya kare martabar kayan da Amirka ke kerawa. Wannan matakin dai zai fi shafar Jamus a matsayinta na kasar da kera motocin. Kan batun na kasuwanci tsakanin Turai da Amirkan dai kasashen na EU sun yi magana da murya guda, inda gabanin zaben na tsakiyar wa'adi a Amirkan shugaban Hukumar Tarayyar Turai Jean-Claude Juncker ya bukaci da su cimma wata yarjejeniya da za ta hana karin kudin fito har zuwa tsahon wani lokaci.