Zaben shugaban kasa a Haiti
November 28, 2010Talla
A kasar Haiti a yau ake gudanar da zaben shugaban kasa wanda akansa yan takara 19 zasu kara a zagaye na farko domin maye gurbin Shugaba Rene Preval wanda ya kammala wa'adin mulkinsa. Masu aiko da rahotannin sun ce daga cikin yan takara da ake da su babu wani wanda ake tsamanin zai samu gagarumin rinjaye tun a zagayen farko a la dole sai an kai ga yin zagaye na biyu.
Ana gudanar da wannan zabe ne dai bayan girgizar kasa da ta kashe mutane 1 230 sanan kuma ga cutar amai da gudawa ta kwalara da ta hallaka sama da mutane dubu daya kawo yanzu.
Mawallafi :Abdourahamane Hassane
Edita : Abdullahi Tanko Bala